Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Garkuwa da mutane: Ƴan Kasuwar Kwari na tattara kuɗin fansa

Published

on

Ƴan Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano sun fara tattara kuɗi domin fanso wasu ƴan Kasuwar da aka yi garkuwa da su.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ƴan kasuwa masu saro kaya daga Aba Alhaji Mukhtar Sani ya bayyana hakan ga Freedom Rediyo.

A cewar sa, ƴan bindigar sun nemi diyyar miliyan 25 wanda yanzu haka ƙungiyar ta fara tattara kuɗin.

Dangane da jami’an tsaro Alhaji Sani ya ce, sun sanar da su domin suma su yi nasu ƙoƙarin.

Sai dai hakan ba zai hana su ci gaba da tattara kuɗin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!