Jigawa
Gazawar maza ce ke tilasta mana ɗora wa ƴaranmu talla – Iyaye mata
Iyaye mata a jihar Jigawa sun zargi mazajensu da bada gudummuwa wajen tilasta tura yayansu talla.
Mafi yawa dai mata ne suka fi shiga hatsarin talla a yankunan birane.
Wata uwa da Freedom Radio Dutse ta zanta da ita ta dora laifin tallan da su ke dora wa yayan su a kan iyaye maza.
“Abin da ya sa mu ke dora musu talla, saboda maza sun gaza sauke nauyin da Allah ya dora musu, sun sakar mana, don haka ya zama dole mu nemi mata” a cewar ta.
Ita kuwa wata uwar cewa ta yi “Ai talla ya zama dole domin ta haka ne su ke rufawa kansu asiri na al’amuran yau da gobe”.
Mafi yawa dai ana samun rahotannin cin zarafin yaya mata musamman ta dalilin talla baya ga illar hakan ta bangaren rashin samun ingantaccen ilimi.
You must be logged in to post a comment Login