Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gen Dambazau ya arce daga hannun Anti Kwarafshin

Published

on

Shugaban hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta Kano Janaral Idris Bello Dambazau ya tsere daga hannun jami’an Anti Kwarafshin.

Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano Barista Mahmud Balarabe ne ya bayyana hakan a yau.

Ya ce, suna gayyaci Dambazau ne kan zargin da ake masa na karɓar cin hanci daga hannun mutane daban-daban.

Ana tsaka da bincike sai ya nemi izni cewa zai je ya sha magani, sai aka haɗa shi da ƴan sanda, daga nan sai ya arce, inji Barista Balarabe.

Balarabe Mahmud ya ce, bai gamsu da bayanan da Dambazau ya yi ba, a don haka za a ɗauki mataki na gaba a kansa.

Freedom Radio ta so jin ta bakin Janaral Dambazau amma bai ɗauki kiraye-kirayen wayar da aka masa ba.

Sannan mun aike masa da saƙon karta-kwana amma har kawo lokacin haɗa wannan rahoto babu amsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!