Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasar Kano: Alhajin Baba ya koma APC

Published

on

Majalisar dokokin Kano ta ce ɗan majalisar jihar mai wakiltar Birni Salisu Maje Ahmad Gwangwazo ya sanar da ita ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran majalisar Malam Uba Abdullahi ya fitar a yau Jumu’a.

Sanarwar ta ce, Maje Gwangwazo ya aike wa da shugaban Majalisar Engr. Hamisu Ibrahim Chidari wasiƙa inda ya sanar da shi ficewar tasa.

Gwangwazo ya ce, ya fice daga PDP ne saboda rabuwar kai da rikicin cikin shugabancin da ya dabaibayeta.

A nasa ɓangaren Shugaban Majalisar Engr. Hamisu Chidari ya taya ɗan majalisar murnar dawowa APC, tare da tabbatar masa cewa sun zama uwa ɗaya uba ɗaya, za su ci gaba da aikin ciyar da jam’iyyar gaba.

Chidari ya kuma yaba wa Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da shugaban jam’iyyar na Kano Alhaji Abdullahi Abbas kan ƙoƙarinsu wajen haɓaka jam’iyyar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!