Jigawa
Gidaje da gonaki sama da dubu 50 ne suka lalace a Jigawa – SEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa SEMA ta ce a kalla mutane ashirin ne suka rasa rayukan su yayin da gidaje da gonaki sama da dubu hamsin suka lalace a jihar Jigawa sakamakon mamakon ruwan sama a makon jiya.
Sakataren hukumar Yusuf Sani Babura ne ya bayyana hakan a jiya Litinin lokacin da ya ke bada rahoton yadda aka samu annobar ta ambaliyar ruwa a daminar bana.
Yace ambilayr ruwa daya ce daga cikin kananan hukumomin sha bakwai cikin ashirin da bakwai da aka yi hasashen samun ambaliyar ruwa a jihar Kano wanda kuma yayi sanadiyyar lalata matsunan al’umma da dama.
Hukumar ta kuma ce a damunar bana a kalla gidaje da gonaki dubu hamsin ne ruwa yayi sanadiyyar su.
You must be logged in to post a comment Login