Labarai
Gidauniyar Widi Jallo ta kaddamar da Rijiyar Burtsatsen ta 500 da ta samar
Masana ilimin muhalli da zamantakewar dan Adan sun ce samar da tsaftataccen ruwa ga al’umma zai rage yawan cutuka da ake samu.
Dakta Musa Abdullahi Sufi masanin muhalli a nan Kano kuma malami a Jami’ar Maryam Abacha ne ya bayyana hakan lokacin da gidauniyar tallafawa mabukata ta Widi Jallo ke kaddamar da rijiyar Burtsatse ta dari biyar da suka samar a fadin kasar nan harma da makwabtan kasashe a gidan adana namun daji na Zoo.
An kaddamar da aikin ne a ranar Talata 28 ga watan Janairun shekarar 2025.
Darka Musa Abdullahi Sufi ya kuma ce idan har ganyayyakin da dan adam ke ci suna samun tsaftataccen ruwa za a rage yawan cutukan da ake fuskanta.
Ya kuma ce dukkan mahallin da ya wadata da ruwa maitsafta za a samu kowanne irin ci gaba da ake bukata a cikin sa.
Da yake jawabi yayin kaddamar da gina rijiyar Burtsatsen ta dari biyar a gidan adana namun dajin na Zoo shugaban gidan Kwanzabeta Sadik Kura Muhammad cewa yayi, za su ci gaba da kulla alaka da gidauniyar ta Widi tare da godemata kan abin da take na tallafawa mabukata.
Ita kuwa ana ta jawabin shugabar tsare-tsaren ayyukan gidauniyar Hajiya Bilkisu Hamisu Mai iyali godewa alumma ta yi kan yadda suke basu hadin kai wajen gudanar da ayyukan su.
A nasa jawabin shugaban gidauniyar ta Widi Jallo Alhaji Abubakar Widi kira ya yi ga al’umma da su ci gaba da basu hadin kai.
Gidauniyar ta Widi Jallo dai ta gina rijiyoyin Burtsatse dan tallafawa mabukatan da basu da ruwa a jihohin kasar nan da wasu daga cikin kasashen makwabta.
You must be logged in to post a comment Login