Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Yadda wasu jama’ar unguwa ke tallafawa asibiti domin al’umma a Kano

Published

on

Duk da kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da rabon albarkatun kasa daidai gwargwado, har yanzu ana samun banbance-banbance wajen kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko Wanda akafi sani da sha ka tafi ko kuma primary health care a turance.

Daga cikin kulawar da ake bayarwa a kowace cibiyar lafiya a matakin farko sun haɗa da rigakafi da maganin cututtukan masu yaɗuwa,  kula da lafiyar  mata da yara, tsarin iyali, ilimin lafiyar al’umma, ilimin kula da lafiyar muhalli da tattara bayanan ƙididdiga kan abubuwan da suka shafi lafiya da sauransu.

Saidai cibiyoyin lafiyar kasar nan har yanzu na fuskantar matsaloli da dama Wanda ke kawo koma baya ga cigaban lafiyar al’umma, da hakan ke sanya  mazauna yankunan zuwa wasu asibitocin dake makwabtaka dasu.

Irin wannna kalubale Cibiyar lafiya a matakin farko ta Balarabe Chiroma dake unguwar Rijiyar Zaki gabas a karamar hukumar ungoggo  ke fuskanta wanda mafi yawan cibiyoyin a kasar nan ke ciki ahalin yanzu

Cibiyar dai nada karancin samar da muhimman aiyukan kula da lafiya, rashin isassun kayan aiki, ƙarancin ma’aikatan lafiya , da kuma rashin kyawun muhalli, na asibiti da kuma  rashin samar da isassun magunguna.

Akalla akan duba marasa lafiya da kuma mata masu zuwa awo 150 Akowacce rana a wannan cibiya, ko isassun bencinan zama na zaman marasa lafiya basa isa, bayaga lalacewa da sukayi.

A wata tattaunawa da Abdullahi Jibril Maikano sakataren kwamitin cigaban kungiyar Rijiyar Zaki, ya ce asibitin ya dade yana fuskantar matsaloli da dama , domin ko  rufin asibitin ya kanyi  yoyo a lokutan damuna ,ga matsalar Na’urorin aiki gami da karancin kayan aiki a dakin gwaje -gwaje inda yace hatta Tankunan da ke ba da ruwa ga Asibitin ya lalace.

An tabbatar da cewa nasarar aiwatar da cibiyar lafiya a matakin farko a kowace ƙasa yana buƙatar kasafun isassun kuɗi daga gwamnati , tareda  haɗin gwiwa daga sauran bangarorin da ke da alaƙa da kiwon lafiya irinsu ƙungiyoyin al’umma da kuma masu zaman kansu.

 

Duba da irin kalubalen da Balarabe Chiroma PHC ke fuskanta, Ƙungiyar Ci gaban Rijiyar Zaki tayi hobbasa na tattara kudi tareda tallafi daga Gidauniyar Aisha Buhari domin gyara Asibitin.

Daga cikin kayayyakin more rayuwa da Gidauniyar Aisha Buhari takai cibiyar sun hadar da, gadajen haihuwa, teburan zama na marasa lafiya, kujeru, fankoki, gadajen kwanciya, labule gami da fente musu Asibiti, yayin da ƙungiyar ci gaban Rijiyar Zaki ta basu injin bada hasken lantarki tare da gyara tankunan ruwan Asibitin.

Wasu daga cikin yan unguwar da suke zuwa Asibitin a baya Zainab musa da Halima Bashir sunce a yanzu sunfi jin dadin zuwa sabanin a baya babu kyawun yanayin muhalli Dana kayan aiki Wanda hakan kan tilastasu zuwa Asibitocin waje.

Da al’umma zasu jajarce wajen kulada cibiyoyin lafiya a matakin farko da kansu wajen gyarasu da tallafa musu da kayayyyakin amfani da kuwa an rage matsalolin da Kansanya a fita daga cikin unguwanni domin Neman lafiya.

Wannan rahoto ya samu tallafi daga Sol Solutions Journalism Network, USA da kuma Nigeria Health Watch.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!