Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gine-gine a kan layin wuta ne ya hana inganta lantarki a Kano — Minista

Published

on

Ministan lanrarki na ƙasa Injiniya Abubakar D. Aliyu yace gine-ginen da mutane suke yi a hanyar layin wutar lantarki ne ya kawo jinkirin aikin da gwamnatin tarayya ke yi don karawa da inganta wutar lantarkin da ake samu a Kano.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar aiki da ya kai tashoshin raba wutar lantarki da gwamnati ta gina a Kumbotso da Rimin Zakara dake Kano.

Injiniya Abubakar D. Aliyu yace gwamnati tana son ƙara yawan lantarki da Kano ke samu zuwa megawatt 2000 amma an kasa yin hakan saboda mutane sun gina gidaje a hanyar da babban layin wutar lantarkin zai bi.

Yayin ziyarar ministan ya kuma zagaya tashar lantarki ta Dan Agundi tare da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda ya bayyanawa gwamnan bukatar sa baki domin ganin an kawar da gidajen da suka yi kutse a kan layin lantarkin daga Kumbotso zuwa Dan Agundi.

A nasa martanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatin Kano zata ɗau mataki na kawar da duk waɗanda suka yi gine-gine a kan layin wutar lantarkin domin ganin cewa Kano ta zama babbar cibiya ta raba wutar lantarki.

Ministan lantarkin ya kuma ƙara da cewa, babbar tashar lantarki da ke Rimin Zakara zata bada damar ƙara yawan wutar lantarki da ake samu a jihar Katsina.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa domin ganin maida Kano wata babbar cibiya ta rarraba wutar lantarki a Nijeriya.

Yace yanzu haka Gwamnatin Shugaba Buhari tana gudanar da wani shiri tare da hadin gwiwar kamfanin Siemens na Jamus domin ingantawa da kara yawan mutar lantarki da ƴan Nijeriya ke samu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!