Kiwon Lafiya
gobara ta kone ta kone shagunan sayar da abinci a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano
Wata gobara da ta tashi a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano ta kone shagunan sayar da abinci da sauran kayayyaki tare da haddasa asarar dukiya mai tarin yawa.
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne a daren larabar da ta gabata bayan sallar Magriba a bangaren masu sayar da abinci na makarantar dake titin Yahya Gusau.
A cewar su, sun hango tashin hayaki ne kafin daga bisani wutar ta bazu zuwa sassan kantinan sayar da abincin da sauran kayan masarufin kwalejin.
wasu daga cikin masu gudanar da sana’ar sayar da abinci a makarantar wadanda gobarar ta lashe dukiyar su, sun bayyanawa Freedom Radio cewa gobarar ta yi musu kazamar barna ta dukiyoyi da runfunansu.
A nasa bangaren, Daraktan Makarantar Dakta Musa Gambo, ya ce ya zuwa yanzu, ba a gano musabbabin tashin wutar ba.
Daga bisani an samu nasararkashe wutar da taimakon jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano.