Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta kone tashar NTA a jihar Kwara

Published

on

Wasu bangarori uku a tashar gidan telebijon na kasa NTA dake jihar Kawara sun kama da wuta sakamakon wutar lantarki mai karfin gaske da aka dawo da ita, da misalin karfi goma sha daya na dare.

Wannan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannan Jami’in hulda da Jama’a na gidan talabijin na jihar Kwara Hassan Adekunle.

A cewar sanarwar, ofishoshi Ashirin da takwas ne suka kone tare da lalata muhimman takardu da dama.

Sanarwar ta kuma ce, ma’aikatar gidana telebijon din sun samu nassarar  kashe gobara ce da taimakon hukumar kashe gobara ta jihar Kwara.

Ta cikin sanarwar, gwamnnar Jihar Abdulraman Abdulrazak ya bukaci al’ummar jihar da su rungumi dabi’ar kashe makunnan wuta don kiyaye aukuwar gobara a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!