Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane su tsare kansu, saboda gwamnati ba zata iya ba – ‘Dan majalisa a Kano

Published

on

Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Danbatta Murtala Musa Kore, ya ce al’umma suyi shiri domin kare kansu domin kuwa gwamnati ba zata iya kare al’umma ba.

Murtala Kore ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Alhamis a zantawar sa da Freedom Radio, kan kubutar da ‘yar sa tayi daga hannun masu garkuwa da mutane a daren Talata.

“Ina rokon gwamnatoci su samarwa jami’an tsaro kayan aiki domin yakar ‘yan ta’adda, wannan aiki yafi karfin gwamnatin tarayya ita kadai ya kamata gwamnoni su shiga ciki don taimakawa jami’an tsaro” a cewar sa.

A daren Asabar ne dai, masu garkuwa da mutane su kayi awon gaba da ‘yar ‘dan majalisar Juwairiyya Murtala mai shekaru 17 a gidansu dake garin Kore na karamar hukumar Danbatta, wanda kuma ta samu kubuta daga hannun su a daren Talata.

Karin labarai:

Kwana daya da harin Bagwai, ‘Yan bindiga sun kara kai hari a Danbatta

Yadda aka yi garkuwa da ‘yar ‘dan majalisar Jiha a Kano

Har yanzu dai, iyalan dan majalisar ba su bayyana adadin kudin da suka bayar ba, sai dai mahaifinta ya ce an dai-daita, haka ma hukumomin tsaro a Kano ba su ce komai akai ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!