Manyan Labarai
Gobara ta tashi a kasuwar GSM ta Alfin a Kano
Wata gobara data tashi a daren jiya a kasuwar waya ta alfin da ke unguwar Ja’em a nan birnin kano.
Gobarar dai tayi sanadiyar asarar dukiyoyi mai dimbin yawa amma babu asarar rai.
Rohotanni sun ce gabaran ta kone mafiya yawan rumfuna da kuma teburan ‘yan kasuwar wanda kiyasun kudaden su ya kai Naira miliyan 40.
A cewar shugaban kasuwar Malam Nazir Gambo gobarar ta tashi ne da misalin karfe sha biyu da da rabi a daren jiya Laraba kuma ta kone ialhirin rufunan ‘yan kasuwar.
Shan dumi lokacin sanyi na kawo gobara – Saidu Muhammad
Gobara ta yi sanadiyar rasuwar iyalai a jihar Kaduna
Ko kun san abinda yasa hukumomin kashe gobara ke fuskantar matsala?
Naziru Z. Gambo ya kuma yi kira ga gwamnati data kawo musu dauki ta hanyar tallafa musu da jari domin kuwa a kalla kasuwar tana da matasa da dama da suke kasuwanci a ciki.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa, gobarar da lankwame fiye da rumfuna 40 da kuma tebura 66.