Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Magance matasalolin Arewa ya dogara kan masu ruwa da tsaki- Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na biyu ya shawarci shuwagabanin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki da kuma al’umma dasu rubanya kokarin su wajen ganin sun magance matsalolin dake ciwa Arewa tuwo-a- kwarya.

Muhammadu Sunusi ya bayyana haka ne ya yin taron yaye matasa karo na farko da kungiyar Arewa Development Support Initiative ta yi wanda aka gudanar a harabar rukunin  Katafaren Kantunan Ado Bayero Mall dake kan titin gidan Zoo a nan kano.

Sarkin yace an bar Arewacin kasar nan a baya a kan ababen more rayuwa na ci gaban kasa da suka hadan da harkokin ilimi da lafiya da noma har ma da ci gaban kasuwanci.

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Marigayi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero yana Kallan wasan kwaikwayon Hankaka

Sarkin askar Kano ya kalubalanci likitoci akan yi wa maza shayi

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa manyan baki da dama sun halarci tar on tare da wasu daga cikin hakiman Sarkin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!