Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gobara ta tashi a makaranta kwanan dalibai ta Kanwa

Published

on

Wata gobara da har yanzu ba’a kai ga gano musabbabin tashinta ba ta kone dakunan kwanan dalibai na karamar sakandaren ‘yan mata dake garin Kanwa a karamar hukumar Madobi a nan Kano.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Malam Muhammad Sunusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana hakan, yana mai nuna alhininsa da faruwar lamarin ta yadda wutar ta yi asarar dukaya mai yawa.

Wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fitar, mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf, ta bayyana cewa Kwamishinan ilimi ya umarci sashen kula da gine-gine da ya dauki matakin da ya kamata don shawo kan lamarin.

Ku kalli wasu daga cikin hotonan gobara da tashi a kasuwar GSM ta Afin

Allah ya yiwa shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano rasuwa

Gobara ta yi sanadiyar rasuwar iyalai a jihar Kaduna

Babban jami’i a ma’aikatar kananan hukumin jihar kano bwanda kuma shi ne ya zagaya da Kwamishinan wurin da lamarin ya faru Malam Nasiru Yusuf, ya bayyana har yanzu ba’a kai ga gano musabbabin tashin wutar ba.

Ya kuma ce wutar ta lakume duk wani abu dake cikin dakunan kwanan daliban mai dauke da katifu dari uku, amma dai babu asarar rai ko jin rauni daga bangaren daliban ko ma’aikata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!