Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta lalata dukiyoyi masu yawa a Kano

Published

on

Wata gobara da ta tashi da Unguwar Tudun Maliki dake nan birnin Kano, ta yi sanadiyar Asarar dukiyoyi masu tarin yawa, tare da lalata wasu gidaje biyu.

Shaidun gani da ido sun ce, gobarar ta shafe sama da awanni biyu tana ci, kafin daga bisani jami’an hukumomin kashe gobara ta Jihar Kano da takwararta ta tarayya su samu nasarar shawo kanta.

Freedom Rediyo ta zanta da wasu daga cikin wadanda gobarar ta Konawa gidaje, inda suka bayyana cewa gobarar ta tashi ne a jiya Lahadi bayan sallar Magriba.

Hukumar kasha gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin inda mai magana da yawun hukumar, Nura Abdulkadir Mai Gida ya ce kawo yanzu zuwa babu wanda ya jikkata sanadiyar gobarar.

Wakilan mu Abba Isah Muhammad da Hauwa Mahmoud Wali wadanda suka kai ziyara wajen da lamarin ya faru, sun ruwaito cewa, mazauna unguwar ta Tudun Maliki Sun ba da gudunmawa wajen takaita illar da gobarar ka iyayi musamman wajen tsallakawa makotan gidaje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!