Connect with us

Labarai

Gombe: Yan sanda sun dawo da dokar taƙaita amfani da babura

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ta sanar da dawo da dokar taƙaita amfani da babura a cikin birnin Gombe daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

 

Rundunar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da jami’inta na hulda da jama’a DSP Buhari Abdullahi, ya fitar a Alhamis din makon nan.

 

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne bayan wani taron tsaro da aka gudanar tare da hukumomi da masu ruwa da tsaki domin nazarin halin tsaro a jihar.

 

Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki daga yau Juma’a 3 ga watan Afrilu, 2026 domin dakile ayyukan laifi da ake aikatawa ta hanyar amfani da babura.

 

Rundunar ta bukaci al’umma su bi umarnin tare da bada hadin kai domin tabbatar da tsaro.

 

Sanarwar ta kuma bukaci mazauna jihar su kasance masu sanya ido tare da sanar da duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!