Labarai
Goodluck Jonathan ya isa birnin Accra don halartar taro
Tsohon Shugaban Ƙasar nan Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Dumokaradiyya na Democracy Dialogue na 2025 da Gidauniyar sa ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin ƙasar.
Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya ta mutu”, zai haɗa shugabanni da masana don tattauna ci gaba, ƙalubale, da makomar dimokuraɗiyya a Yammacin Afirka.
Jonathan ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta ƙarfafa dimokuraɗiyya a yankin tare da kawo zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci.
Taron ya zama muhimmin dandali a kowace shekara a Yammacin Afirka da yake tattauna makomar dimokuraɗiyya, inda a baya ya kan jawo ’yan siyasa, ƙungiyoyi, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.
A wannan karon ana sa ran waɗan da za su halarci taron za su tattauna muhimman batutuwa da suke damun yankin.

You must be logged in to post a comment Login