Labarai
Gwamna Abba Gida-Gida Ya Ƙaddamar da Horar da Jami’an Tsaro 2,500
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da horas da jami’an tsaro 2,500 a ranar Lahadi 24 ga watan Disamba 2023 da cibiyar tsaro ta Cooperative Security ta samar da take ƙaramar hukumar Gabasawa.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda da Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Hakan dai na zuwa ne domin cika ɗaya daga cikin alkawurran da gwamnan yayi yayin yakin neman zabe na samar da guraben ayyukan yi ga matasa a jihar da kuma karfafa tsaro na jihar.
Da yake jawabi ga wadanda suka samu horon da sauran masu hannu da shuni a filin wasa na Sani Abacha, Gwamna Yusuf ya ce za a tura jami’an tsaro da aka horas zuwa ma’aikatu hukumomi domin tallafa wa tsarin tsaro a kasa domin inganta tsaro.
Gwamnan ya bukaci wadanda suka samu horon da su jajirce wajen bayar da horon domin cimma burin da aka sa gaba tare da tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bullo da shirye-shirye da za su inganta rayuwar matasa domin aiwatar da ayyukan ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar.
“Ina so in tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancina za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jiharmu ta Kano,” in ji Gwamnan. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya godewa al’ummar jihar bisa hakuri da goyon baya da hadin kai da suke yi da gwamnatinsa tun daga lokacin da aka kafa ta, tare da fatan dorewar ta har zuwa karshen wa’adin ta domin ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa masu tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar jihar.
You must be logged in to post a comment Login