Labarai
Gwamna Abba Gida-Gida ya aza harsashin aikin gadojin Tal’udu Ɗan Agundi
Gwamnan Kano Ya Kaddamar da aza har sashin aikin gadar Ɗan Agundi da Tal’udu.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin ginin gadojin sama da za’a kashe Naira biliyan 27 a mahadar Dan’agundi, da shataletalen Tal’udu duk a cikin birnin Kano.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata takarta da Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamna Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya kuma rabawa manema labarai.
A wajen aza harsashin ginin, gwamnan ya ce an fara gudanar da manyan ayyuka ne domin rage cunkoson ababen hawa, da saukaka tafiye-tafiye, da kawata birnin, da hana gurbatar muhalli, da samar da ababen more rayuwa.
Yayin da yake aza harsashin ginin, Gwamnan ya nanata alkawuran gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar tare da kudurin samar da karin ribar dimokuradiyya musamman ga wadanda aka zalunta.
Ya ce Kano a matsayin ta na babbar birni ta cancanci a samar da gagarumin sauyi na ababen more rayuwa domin biyan bukatun mazauna birane sama da miliyan goma da inganta zamantakewa da tattalin arzikin mazauna birnin.
Ya ci gaba da cewa, kasafin kudin shekarar 2024 da ya riga ya sanya wa hannu ya zama doka an ba shi fifiko kan manyan ayyuka da zai dauki kaso 60 cikin dari.
Alh Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga dan kwangilar da ke gudanar da aikin da ya tabbatar da kammala aikin a kan lokaci, bin ka’idojin kwangila, amfani da kayan aiki masu inganci domin gwamnati ba za ta amince da aikin da bai dace ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a kan yadda ake gudanar da ayyukan samar da kudaden yana mai cewa ya kasance al’ada ce daga magabata na samar da irin wadannan manyan ayyuka ta hanyar asusun hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke gudanarwa.
Ya kuma yi kira ga mutanen da ke amfani da hanyoyin aikin da kuma na kusa da wuraren da su yi hakuri kan rashin jin dadin ayyukan da ka iya haifarwa tare da tabbatar da cewa ana shirin samar da wasu hanyoyin da za a bi domin saukaka zirga-zirga.
You must be logged in to post a comment Login