Labarai
Gwamna Abba Gida-Gida zai fara raba kayan abinci ga jama’a ran Litinin
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce ran Litinin mai zuwa za’a ƙaddamar da rabon bayar da kayan abinci ga al’umma jihar nan domin rage matsin rayuwa da al’umma suke ciki inda yace za’a fara bayar da kayan abincin ne da ƙananan hukumomin cikin birni
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin taron tattaunawa da gamayyar kwamitocin Lafiya Jari, CRC, Kano Profer, Kwankwasiyya domin tattaunawa kan yadda za’a ci gaba da samar da hanyoyin da za’a taimaka al’umma
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce ranar Litinin mai zuwa za’a kai kayan filin wasa na Sani Abacha domin rabawa ga shugabannin da zasu zagoranci raba shi a ƙananan hukumomin na cikin birni
Ka zalika Gwamnan ya kuma ce zasu bayar da tallafi ga mata 4440 da suke dukkan ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar da jari domin yin sana’o’in dogaro da kai
Inda ya buƙaci nan take da a kawo sunayin mata Goma Goma daga dukkan mazaɓun jihar kano domin bayar da jari da zasu fara sana’a
Haka kuma gwamnan Abba Kabir Yusuf ya ce zasu samarwa da masu buƙata ta musamman suma wani tsari na tallafi da zai tallafa musu wajen yin sana’o’in da zasu dogara da kan su
Inda yace suma ana sane da su domin suma sun bada gudunmawa yadda ya dace dan haka dole gwamnati ta kyautata musu
Haka kuma Abba Kabir Yusuf yace za’a samarwa da matasa suma 4440 jarin da zasuyi sana’o’i da zasu riƙe kan su da kuma samarwa da ƴan adaidai Sahu motocin taxer na Amana domin ƙara samarwa da matasa sana’o’i
Haka kuma za’aje dukkan Dam ɗin da suke jihar Kano domin gyara su domin ƙara bunƙasa harkokin noma a jihar Kano
Gwamnatin tace zata cigaba da samar da hanyoyin da sa’a samarwa da matasa hanyoyin sana’o’i na dogaro da kai
You must be logged in to post a comment Login