Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya aika wa majalisa sunan jami’an riƙo na ƙananan hukumomi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya aike wa majalisar dokokin jihar Kano sunayen mutanen da za su jagoranci shirya zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe.

Ta cikin wasiƙar gwamna Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ta tantancewa tare da amincewa da mutanen da ya ke son naɗawa a matsayin jami’an riƙo na ƙananan hukumomi.

Shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ne ya karanta wasiƙar a zaman majalisar na yau.

A nasa ɓangaren, shugaban masu rinjaye na zauren Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ya yi ƙarin haske kan wasiƙar, ya na mai cewa doka ce ta tanadi yadda za a naɗa mutanen da za su kula da ƙanannan hukumomi yayin da wa’adin zaɓabbu ya ƙare.

Bayan amincewa da buƙatar gwamnan, majalisar dokokin ta umarci waɗanda gwamnan ya tura da sunayen nasu da su ke majalisar a gobe Laraba da misalin ƙarfe 12:00 domin tantance su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!