Labarai
Gwamna Abba Kabir ya buƙaci majalisa ta sahale masa kafa cibiyar yaki da cutuka
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci majalisar dokoki da ta amincewa domin ya kafa cibiyar yaki da cututtuka masu yaɗu.
Gwamnan ya buƙaci hakan ne ta cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar wadda shugabanta Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya karanta yayin zaman majalisar na yau Litinin.
Ta cikin wasiƙar, gwamnan ya bayyana cewa, kafa cibiyar zai tai wajen magance bullar cutar da kuma daƙile barkewar annoba.
A dai zaman na yau majalisar ta karɓa tare da amincewa da rahoton kwamitinta na harkokin zaɓe dangane da tantance Farfesa Sani Lawan Malumfashi da gwamnan ya aike da sunansa domin naɗa shi a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC wanda shugaban masu rinjaye na zauren Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa ya gabatar.
Yayin gabatar da rahoton, Lawan Hussaini, ya ce, a tantancewar da suka yi wa Farfesa Malumfashi, sun gano cewa ya cancanci riƙe muƙamin.
You must be logged in to post a comment Login