Labarai
Gwamna Abba Kabir ya buƙaci NBC ta fara tantance kafafen yaɗa labarai na Internet

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci hukumar da ke kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ta fara tantance kafafen yada labaran Internet.
Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a taron da Hukumar NBC ta shirya a birnin Legas, wanda ya hada masana, masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin kafafen yada labarai, inda ya ce ya kamata NBC ta fara tantance kafafen rediyo da talabijin na intanet don dakile yada labaran karya da kalaman batanci a kafafen sadarwa.
Gwamnan wanda Daraktan yada labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wakilta, ya nuna damuwa kan yadda wasu kafafen intanet ke yada labarai marasa tushe musamman wadanda ke da nasaba da addini ko siyasa.
To sai dai tun a baya NBC ta sha bayyana cewa dokarta ba ta bata wannan damar ta tantance kafafen rediyo da talabijin na intanet ba.
You must be logged in to post a comment Login