Labarai
Gwamna Abba Kabir ya dauki daliban da suka kammala karatu a Cyprus aiki

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya dauki daliban da gwamnatin Kano ta kai su karatu kasar Cyprus su 84 aiki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Alhamis din makon nan yayin da ya ke mika musu shaidar kammala karatu a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati.
Daliban dai, sun kammala karatun tun a shekarun baya, amma ba su samu karbar shaidar kammalawa ba saboda rashin biyan cikon kudaden karatunsa, wanda gwamnan ya kammala biya a kwanakin baya.
You must be logged in to post a comment Login