Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya miƙa ta’aziyyar sa ga Kwamishinan Ruwa na jihar Kano

Published

on

Gwamanan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa ta’aziyyar sa ga Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Ali Haruna Makoɗa bisa rasuwar ƴar sa Usaiba Ali Haruna Makoɗa da tayi jiya bayan fama da jinya.

Gwamna Abba ya miƙa saƙon ta’aziyar ta cikin wani saƙo da sakataren yaɗa labaran sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya rabawa manema labarai

Gwamnan kuma ya mika ta’aziyya ga iyalai, da ƴan uwanta tare da addu’ar Allah maɗaukakin Sarki da ya jiƙan ta da rahama, ya bada ikon jure rashin ta, ya kuma albarkaci yaron da ta bari.

Marigayiyar dai ita ce babba a cikin ƴaƴan Ali Haruna Makoda, kuma ta rasu ne bayan jinya ta ‘yan makonni bayan ta haifi danta na farko.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!