Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Gwamna Abba Gida-Gida ya taya al’umma murnar zagayowar watan Maulidi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar jihar murnar zagayowar watan haihuwar ma’aiki SAW

Hakan na cikin wani saƙo da sakataren yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya kuma rabawa manema labarai

Gwamna Abba Kabir, ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmai da suyi koyi da irin kyawawan ɗabi’un Manzon Allah SWA da Sahabban sa wajen haƙuri san juna tausayi domin neman dacewa a rayuwa

Gwamnan ya kuma buƙaci al’ummar musulmai musamman matasa da su dunga karanta Tarihin ma’aiki da Sahabbai wanda hakan zai tallafa musu a dukkan bangarori na Rayuwar su kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Ya kuma shawarci al’umma da suyi anfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin samin sauƙin matsin rayuwa da samar da tsaro a faɗin jihar

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!