Labarai
Gwamna Abba Kabir ya tafi Saudiyya don halartar jana’izar Aminu Dantata

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya tashi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano tare da manyan jami’an gwamnati domin halartar jana’izar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan biyo bayan wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
Tawagar da ta tafi zuwa jana’izar ta haɗa data Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi da Khalifa Muhammadu Sanusi II.
Haka zalika akwai tsohon gwamnan Jigawa, Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu manyan sarakuna da jami’an gwamnati daga Kano da Jigawa.
Daga cikin wadanda suka shiga tawagar har da Galadiman Kano,sai Matawallen Kano, da Sarkin Yakin Kano, sai Injiniya Sagir Koki, Nastura Ashir Sharif, Alhaji Sabiu Bako.
You must be logged in to post a comment Login