Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a kamo tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, bisa zargin haifar da tashin hankali a jihar.

A daren jiya ne dai aka shigo da tsohon Sarkin cikin birnin Kano a yunkurinsa na komawa fadar da karfi, bayan kwana biyu da Gwamna ya sauke shi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, an tabbatar da cewa sabon sarki Sanusi Lamido Sanusi ya isa fadar ne tare da gwamnan jihar da mataimakin sa tare da kakakin majalisar dokokin jihar da sauran manyan jami’an gwamnati da misalin karfe 1:00 na safe ranar Asabar, 25 ga Mayu, 2024.

mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umurci kwamishinan ƴan sanda da ya kamo sarkin da aka tsige ba tare da bata lokaci ba saboda tada hankalin al’umma da yunkurin lalata zaman lafiya. jiha.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!