Labarai
Gwamna Abba Kabir ya yi wa wasu manyan jami’an gwamnati sauyin Ma’aikatu

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauya wa wasu manyan jami’an gwamnatinsa ma’aikatu.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a daren Litinin ɗin makon nan, inda ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na ƙarfafa shugabanci da inganta ayyukanta.
A sabon sauyin, an mayar da Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isa Dederi, zuwa Ma’aikatar Sufuri.
Haka shi ma Babban Lauyan Gwamnati kuma Sakatare a Ma’aikatar Shari’a, Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad, an yi masa sauyi zuwa Ma’aikatar Muhalli a matsayin babban Sakatare.
Kwamishinan Harkokin Jinƙai, wanda ya kasance na rikon kwarya a Ma’aikatar Sufuri, zai koma ma’aikatarsa ta Jinƙai.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan jami’an da sauyin ya shafa da su mika mulki ga manyan jami’an ma’aikatunsu a yau Talata, 23 ga Satumba.
ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na da cikakken kishin tabbatar da gaskiya, inganci da shugabanci na gari. Ya ce wannan sauyin an yi shi ne domin amfani da ƙwarewa yadda ya kamata,da kuma daidaita aiki, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta na kai wa ga matakin nasara wajen sauke nauyin da al’umma da suka dora mata.
Ya kuma yi kira ga dukkan jami’an gwamnati da su ba da cikakken haɗin kai ga kwamishinoni domin su gudanar da ayyukansu yadda ya dace.
You must be logged in to post a comment Login