Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamna Ganduje  ya kafa kwaimitin mika mulki ga Abba Kabir Yusuf

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamitin miƙa mulki ga zaɓaɓɓen Gwamnan jiha Engr. Abba Kabir Yusuf.

A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce Kwamitin na ƙarƙashin shugabancin Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji.

Sai kuma wasu Kwamishinoni da manyan jami’an gwamnati da kuma wakilci daga ɓangaren sabon zaɓaɓɓen Gwamnan.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da sabon zaɓaɓɓen gwamna ya ƙaddamar da nasa Kwamitin na karɓar mulki.

Jihar Kano dai na cikin jihohin da siyasarta ke ci gaba da ɗaukar ɗumi sakamakon samun sauyin gwamnati da za a yi daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jami’yyar adawa ta NNPP.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!