Labarai
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya saki fursunoni mata 8

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya saki mata fursunoni takwas daga gidan gyaran hali na Goron-Dutse, inda ya biya musu tara da kuma basussukan da ake binsu.
Daga cikin matan da aka sako, hadda mata masu juna biyu da kuma wasu biyu da ke shayar da jarirai.
Gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai gidan gyaran halin tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya bayyana manufar ziyarar da duba yanayin da fursunonin ke ciki da kuma gano hanyoyin da gwamnati za ta tallafa musu bayan sun fita daga gidan..
You must be logged in to post a comment Login