Labarai
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da kudirin gwamnatin Kano na baiwa bangaren Ilimi fifiko

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da baiwa bangaren ilimi fifiko domin inganta jihar da al’ummar ta baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau yayin bikin murnar Ranar Malamai ta Duniya, da aka gudanar a ofishin ƙungiyar Malamai ta ƙasa (NUT), reshen Jihar Kano.
Da yake isar da saƙon Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ɗauki matakai na ci gaba wajen inganta fannin ilimi da walwalar malamai a faɗin jihar.
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar Malaman Makarantu ta Jihar Kano (NUT), Kwamared Baffa Ibrahim, ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da haɗa kai da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin bunƙasa harkar koyarwa da walwalar malamai.
Taron ya samu halartar malamai, hukumomi, ƙungiyoyi da sauran al’umma masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, domin tunawa da girmama rawar da malamai ke takawa wajen gina al’umma.
You must be logged in to post a comment Login