Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun tabbatar da Muhammadu Sunusi II a matsayin sarkin kano – Gwamna Abba

Published

on

Gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf ya mika wa sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi II shaidar tabbatar da shi a matsayin Sabon Sarkin Kano na 16 a dakin taro na Afrika dake gidan gwamnati.

Wannan ya biyo bayan rattaba hannu da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi kan sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta gabatar masa wadda ta rushe sabbin masarautu hudu da Gwamnatin data gabata ta kirkiro a jihar kano.

Da yake jawabi yayin mika masa shaidar tabbatarwar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon Sarkin ya rike al’umarsa bisa adalci da amana.

Ya Kuma bukaci Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya dora Kan kyawawan halayensa na tausayi da taimakon mabukata tare da hada kan alumar jihar Kano.

A jawabinsa Jim kadan bayan da ya karbi shedar tabbatar dashi a karagar masarautar Kano, Sarki Muhammadu Sanusi Na Biyu ya godewa Gwamnan Abba Kabir Yusuf da majalisar dokokin jihar Kano bisa dawo da kima da martabar Masarautar Kano wadda aka santa dashi tun sama da shekaru dubu daya da suka gabata.

Ya kuma godewa al’umar jihar Kano da sauran masoya daga sassan duniya daban-daban, bisa addu’oi da kauna da suka nuna masa, tare da alwashin hada Kan masarauta da alumar jihar Kano baki daya.

Wannan dai na nufin, yanzu Jihar Kano ta dawo karkashin masarauta daya Kuma mai Sarki daya wato Alhaji Sanusi Lamido Sanusi na biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!