Connect with us

Labaran Kano

Kwamitin yaƙi da shan miyagun kwayoyi na Kano ya yi taro a karon farko

Published

on

Kwamitin Hada Gwiwa na Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safarar Haramtattun Ƙwayoyi ya gudanar da taronsa na farko, inda ya jaddada aniyarsa ta haɗa ƙarfi wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi, safararsu ba bisa ƙa’ida ba, daba da sauran laifukan da ke da alaƙa da su a faɗin jihar.

Shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ne ya jagoranci taron, wanda ya haɗa manyan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da aka ɗora wa alhakin aiwatar da manufofin kwamitin.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tajo Usman; Kwamandan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na jihar, Dakta Mustapha (DAG); Babban Sakataren Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta Jihar Kano; Shugaban Ayyuka na Hukumar Tsaro ta DSS a Kano; Jami’in da ke jagorantar Rundunar Anti-Daba, da sauran mambobin kwamitin.

A jawabinsa, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado ya ce an kafa kwamitin ne domin samar da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi wajen magance matsalar shan miyagun ƙwayoyi da laifukan da ke da alaƙa da ita a jihar Kano.

Ya ce nasarar kwamitin za ta ta’allaka ne kan haɗin kai, kyakkyawar mu’amala tsakanin hukumomin da ke cikinsa, da kuma jajircewar kowane mamba wajen gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa, gaskiya da kishin ƙasa.

Ya kuma buƙaci mambobin kwamitin su mayar da hankali kan aikin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗora musu, yana mai cewa yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu ba bisa ƙa’ida ba na buƙatar musayar bayanan sirri, ƙarfafa aikin doka, wayar da kan jama’a, shirye-shiryen gyaran halaye da kuma ci gaba da aiki tare da al’ummomi.

Barrista Muhuyi ya ƙara da cewa kwamitin zai yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, malamai, ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin matasa da shugabannin al’umma domin samar da ingantattun hanyoyin kare makomar matasan Kano da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

A nasu jawaban, mambobin kwamitin sun bayyana cikakken goyon bayansu ga manufofin kwamitin, tare da jaddada muhimmancin ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, tattara sahihan bayanan sirri, saka al’umma cikin yaƙin da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a domin shawo kan matsalar shan miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke tattare da ita.

A ƙarshen taron, an cimma matsayar ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi, tsara tsarin gudanar da ayyukan kwamitin, da kuma fara aiwatar da matakan haɗin gwiwa bisa umarnin Gwamnatin Jihar Kano.

Kwamitin ya sake tabbatar da kudurinsa na yin aiki ba tare da gajiyawa ba domin gina Kano mai aminci, lafiya da tsaro, tare da yin kira ga al’umma da su ba da sahihan bayanai tare da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da sauran ayyukan ta’addanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!