Labarai
Muna kira ga gwamna Abba ya cika alkawarin da ya dauka na dawo mana da ‘ya’yanmu da aka sace -Kano 9
Kungiyar iyayen Yara ‘Yan Asalin Kano da aka sace zuwa kudancin kasar ta yi Kira ga gwamman Kano da ya cika alkawarin da ya yi musu na sake dawo musu da yaransu 18 da aka sake ganowa
Shugaban kungiyar ta Kano 9 kwamared Ismail Ibrahim Muhammad ya ce yau kusan shekara guda ke nan da gwmnan Kano ya yi musu alkawarin dawo da yaran Amma haryanzu babu labarin.
Itama wata uwa da aka sace Mata yayanta biyu tace gwmnan ya yi Mata alkwarin cewar zai taimaka wajen dawo da yayansu.
A makon daya gabata ne wata kotu a nan Kano ta cigaba da Sauraron Shari’ar da ake yiwa Wanda Ake zargin da satar yaran
You must be logged in to post a comment Login