Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba ya sanya hannu ƙan ƙwarya-ƙwaryar kasafi da yakai biliyan 99

Published

on

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba kabir Yusuf ya sanya hannu kan ƙwarya-ƙwaryar kasafin kudi da ya aike gaban majalisar Dokoki ta jihar, na Naira biliyon Casa’in da tara da miliyan ɗari biyu da ashirin da ɗaya da dubu ɗari biyar da uku da dari biyar da sittin da tara da kobo casa’in da uku (99,221,503,569.93).

Inda Gwamnati ta ware kaso 36 daga cikin dari domin gudanar da ayyuka nayau da kullun, inda kaso 64 zasu karkata kan Manyan Ayyuka.

Gwamnatin ta gabatar da ƙarin kasafin ne domin wasu buƙatu da suka taso mata.

– Haka kuma akwai ƙarin kuɗin mafi ƙarancin Albashi da yatashi daga Naira dubu talatin yakoma dubu saba’in

– haka kuma za’a ɗinkawa tare da rabawa ɗaliban firamare unifom guda dubu dari bakwai, domin bawa kowanne yaro guda biyu.

– Akwai sauran Ayyuka da Gwamnati takebda ƙudirin yi sakamakon hakan dole sai ankai ƙarin kasafin kuɗin indai har ana so ya gudanar saboda tsadar kaya musamman karin kudin man fetur.

– Akwai harkokin zaɓen ƙananan hukumomi da ake shirye shiryen sa a wannab lokacin.

Haka kuma gwamnatin jihar Kano tace zata ci gaba da fito da tsare-tsaren da zasu inganta rayuwar al’umma dake faɗin jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!