Connect with us

Labarai

Gwamna Abba ya yi wa Abdullahi Baffa Bichi martani

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi martani kan zargin da tsohon Sakataren gwamnatinsa jihar Abdullahi Baffa Bichi, da ya yi na cewar ana sata a gwamnatin mai ci fiye da wadda ta gabata ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje. 

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne a wani taron ganawa da zababbun Kansiliolin Kano da ya gudana ranar Lahadi a daki taro na gidan gwamnati.

Gwamnan, ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ba za ta lamunci cin zarafin shugabanin jihar ba, ko yi wa doka karantsaye.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma umarci Kansilolin da su gabatar masa da ayyukan da mazabunsu ke bukata don aiwatar da su tare da fito da matasan da ke bukatar ci gaba da karatu domin gwamnati ta dauki nauyinsu. 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!