Labaran Kano
Gwamna Abba zai koma APC a gobe Litinin

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC, mai mulkin kasa a gobe Litinin 26 ga watan Janairun 2026.
A ranar Juma’a ne gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyarsa ta NNPP, saboda abin da ya bayyana da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar,
Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a jiya Lahadi, ya ce gwamna ya yanke shawarar komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC bayan tuntuɓar abokan shawararsa na siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Abba Kabir Yusuf ya taɓa shiga APC a 2014, in da ya ce sake komawa APC zai ƙara ƙarfafa alaƙa mai ƙarfi tsakanin gamnatin jihar da ta tarayya, wani abu da sanarwar ta ce zai samar wa jihar ci gaba da ƙarfafa tsaro da inganta ci gaban jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar Litinin ɗin gwamnan zai karɓi katin jam’iyyar APC tare da wasu ƴan majalisar dokokin jihar 22 ciki har da kakakin majalisar, da ƴanmajalisar tarayya takwas da shugabannin ƙananan hukumomi 44.
You must be logged in to post a comment Login