Connect with us

Labarai

Gwamna El-Rufai ya gargadi malaman makaranta da su kauracewa bin umarnin kungiyar NUT

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi malaman makaranta da su kaucewa bin umarnin da kungiyar malamai ta NUT ta bayar na tsunduma yajin aiki a yau Litinin.

A yau Litinin 8 ga watan Janairun da muke ciki dalibai a Kaduna ke komawa makaranta bayan kammala hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.

A jiya Lahadi ne kungiyar NUT ta bukaci ‘ya’yan kungiyar su zauna a gidajensu har sai gwamnatin Jihar ta sauya matakin da ta dauka na sallamar malaman Firamare sama da 21,000 daga bakin aiki,sakamakon gaza cin jarrabawar da gwamnatin Jihar ta shirya musu.

A baya can NUT ta baiwa gwamnatin Jiha wa’adin makonni biyu na ta sauya hukuncinta amma har ya kare ba ta sauya ba, inda kuma kungiyar kwadago ta NLC ta koka kan matakin kasancewar maganar na gaban kotu.

Mai magana da yawun gwamna El-Rufai Mista Samuel Aruwan ya jaddada umarnin gwamnatin ga malaman da cewa lallai kada su bi umarnin kungiyar ta NUT.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,889 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!