Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

El-rufa’i ya rushe gidaje sama da 50 a Zariya

Published

on

Hukumar tsara birane ta jihar Kaduna ta rushe gidaje sama da 50 a filin idin bare-bari dake yankin kofar Kona a Zariya.

Cikin wata zantawa da manema labarai, shugaban hukumar tsara birane ta jihar Kaduna wato KSUPDA Ismai’l Dikko, ya ce sun rushe gidajen ne, saboda an gina su ba bisa ka’ida ba, sannan filin idin wuri ne na tarihi, kuma wurin ibada ne, a don haka tilas suyi iya kokari wajen kare wuraren ibada da wuraren tarihi.

Ya kara da cewar, ba suyi wannan rusau ba, sai da suka fara sanar da mutanen yankin tare da basu notis.

Sai dai wasu mazauna yankin da Freedom Radio ta zanta da su, sun ce, basu samu wani notis daga KASUPDA ba, sannan da yawansu sun fara gini ne, bayan da suka samu izni daga KSUPDA, amma katsaham sun wayi gari hukumar ta zo ta fara rushe musu gidaje.

Karin labarai:

Har yanzu lockdown na nan a Kaduna – Inji El-Rufa’i

Gwamna El-Rufai ya gargadi malaman makaranta da su kauracewa bin umarnin kungiyar NUT

A nasa bangaren sarkin yankin Alhaji Abdullahi Dalhatu sarkin Kwagworo ya shaidawa wakilin Freedom Radio Hassan Ibrahim Zariya cewa, rabon da ayi sallar idi a wannan fili, tun zamanin sarkin Zazzau Ja’afaru wanda yau kusan sama da shekaru sittin kenan.

Sarkin Kwagworo ya kara da cewa, tun a lokacin da al’umma suka fara mamaye filin da gine-gine, da ma shi bai goyi baya ba, saboda taka sa katsen dake ciki, a don haka yaki sanya wa masu filayen hannun a takardun su.

Kwamaret Tukur Dan Mu’azu wani mai fafutukar kare hakkin al’umma ne a birnin Zazzau, ya roki gwamnan jihar Malam Nasir El-rufa’i kan yayi duba na tsanake domin yin sassauci ga mazauna wannan yanki.

Ku saurari cikakken labarin, ta cikin wannan rahoton.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!