ilimi
Gwamna Namadi ya bude Makaranta ta musamman a Garki

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, ta kashe sama da Naira miliyan dubu biyar wajen ginawa tare da sanya kayan aiki a Sabuwar makarantar Sakandire ta musamman da ke garin Garki domin koyar da ilimi da kuma Sana’oin dogaro da kai ga dalibai.
Da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron bude makarantar, gwamnan jihar Malam Umar Namadi, ya ce, makarantar ta na daga cikin makarantun Sakandire na musamman guda takwas da gwamnatinsa za ta samar a sassan jihar.
A nasa jawabin, kwamishinan ilimi mai zurfi na Jigawa Farfesa Isah Yusuf chamo ya ce, an zabo daliban makarantar ne bisa cancanta bayan sun samu nasara a jarawar da aka shirya musu har sau uku.
Kwamishinan, ya kara da cewa, bude makarantar wani bangare ne daga cikin shirin gwamnati da jama’a karo na takwas a karamar hukumar ta Garki.
You must be logged in to post a comment Login