Labarai
Gwamna Namadi ya bukaci manyan Najeriya su iya bakin su

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya bukaci manyan Najeriya da su iya bakin su tare da kauce wa yin duk abinda zai haddasa barkewar rikici da wargaza kasa.
Gwamnan ya bukaci hakan ne ta cikin shirin gidan Talabijin na Channels, na Sunrise Daily, yayin da ya ke mayar da martani kan kalaman tsohon ministan tsaron kasar nan Janar Topilus Theophilus Danjuma, da ya umarci al’umma su kare kansu daga ‘yan tada kayar baya da masu garkuwa da mutane.
A cewar gwamna na Jigawa, bai kamata a ce kalaman suna fitowa daga bakin manya ba kamar shi, duba da halin da ake ciki a kasar nan inda ya ce, su ne manyan da za su samar da hanyoyin dakile hakan ko kawo karshen tashe-tsahen hankula.
Idan za a iya tunawa dai a baya-bayan nan ne Janar Topilus Theophilus Danjuma, mai ritaya ya umarci al’ummomin da ke fuskantar kalubalen tsaro musamman ma a jihohin Plateau da Benue da Taraba da su tashi tsaye don kare kansu daga matsalolin tsaro da ke addaabar su.
You must be logged in to post a comment Login