Labarai
Gwamna Radda ya jagoranci takwarorinsa wajen ganawa da babban hafsan soji

Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci wasu gwamnonin yankin wajen ganawa da babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa, a shalkwatar tsaro ta ƙasa da ke Abuja.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa taron na sirri ya mayar da hankali ne kan tsare-tsare da ƙarfafa ayyukan tsaro a Arewa maso Yamma, musamman ganin nasarorin baya-bayan nan da dakarun soji suka samu kan ‘yan bindiga a yankin.
Cikin tawagar da Dikko Radda ya jagoranta har da Gwamnan Zamfara Dauda Lawal da mataimakin gwamnan Sokoto Alhaji Idris Mohammed Gobir da sakataren gwamnatin jihar Kebbi Alhaji Yakubu Bala.
You must be logged in to post a comment Login