Addini
Gwamna Radda ya kaddamar da taron addu’o’i kan matsalolin tsaro

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da shirin addu’o’i na musamman tare da malamai da shugabannin addini da masu rike da sarautun gargajiya domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Wata sanarwra da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ce ta bayyana hakan.
Sanarwar ta ce, taron ya haɗa malamai da shugabannin al’umma da jami’an gwamnati daga sassa daban-daban na jihar, inda aka gudanar da addu’o’i ga waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon matsalar tsaro tare da roƙon Allah ya ci gaba da bai wa jihar kariya daga matsalolin tsaro.
Gwamna Radda ya ce, matsalar tsaro ba ta da alaƙa da addini ko siyasa, inda ya jaddada cewa haɗin kai da hakuri su ne ginshiƙai wajen magance ta.
You must be logged in to post a comment Login