Labarai
Gwamna Zulum ya sauke dukkan Kwamishinoninsa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sauke dukkanin kwamishinoninsa daga mukamin su.
Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da sakataren gwamnati Bukar Tijani ya fitar, ya na mai bayyana cewa Gwamnan ya dauki matakin ne domin bai wa duk mai bukatar tsayawa wata takara ta siyasa dama.
Haka kuma, gwamnan ya yaba musu bisa aikin da suka yi, tare da yi musu fatan alheri a abubuwan da suka saka a gaba.
You must be logged in to post a comment Login