Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Zulum Ya sauke kwamishinan lafiya na jihar Borno

Published

on

Gwaman jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sauke kwamishinan lafiya na jihar Dakta Salihu Kwayabura daga mukaminsa a yau Talata, tare da bukatar shugaban ma’aikatan gwamnatin Farfesa Isa Hussani Marte ya kula da ma’aikatar.

wannan dai na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Malam Isaha Gusau ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce umarnin na gwamna Zulum na daga cikin matakan da suka dace na sake sauya fasalin ma’aikatar.

Gusau ya kuma ce, gwamna Zulum na nuna godiya ga Dakta Salihu Kwayabura kan irin gagarumar gudummawar da ya bayar wajen ci gaban bangaren kiwon lafiyar al’ummar Borno a cikin shekaru biyu da yayi yana jagorantar ma’aikatar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!