Kiwon Lafiya
Gwamnan Benue yace bashi ne ke da alhakin kashe-kashen da ke wakana a jihar ba
Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya ce ba shi ne ke da alhakin kasha-kashen da ke wakana a Jihar ta Benue ba, a don haka ba dai dai ba ne a rika danganta ta shi da ma gwamnatinsa da lamarin.
Samuel Ortom na fadin hakan ne a jiya Talata lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, yana mai cewa rikicin Makiyaya da Manoma ya hallaka mutane da dama, wanda kuma ya janyowa wannan gwamnati abin fade.
Ya kuma ce a cikin Jihar ta Benue akwai Makiyaya masu bin doka da oda, inda kuma a gefe guda ake samun wasu bata-garin daga cikinsu, sannan ya ayyana kungiyar Makiyaya ta Miyetti Al.. a matsayin makiya zaman lafiya.
Gwamna Ortom ya bayyana kungiyar da cewa ita ce ta ke tunzura ‘ya’yanta wajen bijirewa dokokin Jihar na haramta kiwo barkatai, a don hakane ya dora alhakin rikicin a kansu.