Labarai
Gwamnan Gombe ya bayyana kaduwa bisa hatsarin Kwale-kwale a kogin Nafada

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana bayyana kaduwa tare da mika jajensa da ta’aziyyarsa bisa rasuwar wasu matasa da suka sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya faru a kogin Nafada ranar Asabar.
A cikin sanarwar da Daraktan yada Labarai na Gwamnatin jihar, Ismaila Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da takaici, yana mai jaje ga iyalan mamatan da al’ummar Nafada baki ɗaya.
Haka kuma ta cikin sanarwar, gwamnan ya nema wa wadanda suka rasun fatan gafarar Allah tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalansu.
Haka kuma gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukaci mutane da su kara kula da ka’idojin tsaro wajen sufurin ruwa.
Ya kuma umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da hukumar kananan hukumomi su taimaka wa iyalan mutanen da hatsarin ya ritsa da su tare da kuma wayar da kai domin guje wa irin wannan iftila’in a gaba.
You must be logged in to post a comment Login