Labarai
Gwamnan Jigawa ya bukaci DSS ta kai wa Jiharsa dauki
Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya buƙaci rundunar tsaro ta Civil Defense ta ƙasa da ta tura ƙarin jami’anta domin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Olusola Odumosu ya fitar jiya Alhamis a Abuja.
Odumosu, ya ce Gwamna Namadi ya yi wannan roƙo ne yayin wata ziyara da ya kai wa babban kwamandan rundunar Ahmed Audi.
Malam Umar Namadin yace rikice-rikicen dake wakana tsakanin makiyaya da manoma a jihar tsawon shekaru ya durƙusar da harkokin noma a jihar.
Gwamnan ya kuma yi ƙira ga rundunar da ta samar da tsaro ga manoman yankunan da rikicin ya shafa a jihar domin dawo da kwarin gwiwar manoman.
Acewar sa jihar ta na bada gudunmawa sosai wajen samar da abinci ga al’ummar ƙasar nan, kuma yankunan da abin ya shafa sun kasance masu samar da abincin.
Da yake mayar da martani, Audi ya yi alkawarin tura kwararrun jami’an su ƙarkashin atisayen Agro Rangers zuwa jihar domin lalubo hanyoyin magance matsalar.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login