Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dattawa ta magantu kan ambaliya a Nijeriya

Published

on

Majalisar dattawan Nijeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake cigaba da samun asarar rayuka da dukiyoyin al’umma sanadiyar ambaliyar ruwa.

Majalisar ta kuma bukaci Hukumar ba da agajin Gaggawa ta kasa NEMA da ta gaggauta aiwatar da shirin sake tsugunar da al’ummar yankunan da ke fuskantar haɗarin ambaliyar.

Cimma matsayar ya biyo bayan ƙudurin da Sanata Osita Izunaso na jam’iyyar APC daga shiyyar Imo ta yamma ya gabatar.

Izunaso ya yi nuni da cewa, ayyukan ɓatagari da ambaliya sun yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyin da suka haura Naira biliyan 4, tare da jikkata mutane da dama.

Majalisar ta yi ƙira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin aikin gyaran domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiyoyi da kuma lalata muhalli a yankunan da ake samun ambaliyar ruwa a ƙasar nan.

Majalisar Dattawan ta kuma bukaci Ofishin kula da asusun tallafawa muhalli wato EFO da hukumar NEMA kan su haɗa kai wajen ɗaukar kwararrun da suka dace don gudanar da aikin tantancewar tare da ɗaukar matakan da suka dace don shawo kan matsalar a yankunan da ambaliyar ruwan tafi shafa.

A makon da muke bankwana dashi ne dai hukumar ta NEMA ta fitar da wata sanarwar samun Ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar nan 14 ciki har da nan Kano.

 

Rahoton: Bara’atu Idris Garkuwa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!